1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi barazanar kai hari

Gazali Abdou TasawaJuly 11, 2016

Koriya ta Arewa ta yi barazanar yin amfani da karfin wuta kan wata na'urar garkuwar makami mai linzzami da kasar Amirka ke shirin girkewa a Koriya ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1JMkH
Nordkorea Kim Jong-Un
Hoto: Reuters/KCNA

Rundunar sojojoji masu makaman atilare ta Koriya ta Kudun ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Litinin da kuma tashar talabijin ta gwamnatin kasar ta KTR ta yada.

Kazalika Koriya ta Arewar ta gargadi takwararta ta Kudu da cewa idan ta yarda Amirka ta girke wadannan makamai a cikinta, to kuwa ta kwana da sanin zata sha luguden wutar da ba a taba yin irinsa ba.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce Amirka da Koriya ta Kudu suka sanar da shirin girke na'urar garkuwar makaman masu linzzami mai suna THAAD a wani mataki na rigakafin yiwuwar fuskantar hari daga Koriya ta Arewa.