1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta harba tauraron dan Adam

Yusuf BalaFebruary 7, 2016

Aiwatar da wannan aiki da ya sabawa dokoki da dama na Majalisar Dinkin Duniya, na zama wani abu da ke ninkin baninki kan irin laifukan da kasar ke yi.

https://p.dw.com/p/1Hr23
Nordkorea Start von Langstreckenrakete
Hoto: Reuters/Yonhap

Koriya ta Arewa ta bayyana a ranar Lahadin nan cewa ta samu nasara wajen harba tauraran dan Adam dinta da ya samu rakiyar makami mai linzami cikin samaniya, abin da ke samun suka tsakanin kasa da kasa wadanda ke kallon kokarin kasar ta Koriya ta Arewa a matsayin gwajin makami da ke da karfin da zai iya afkawa tsakiyar Amirka idan kasar ta so.

Aiwatar da wannan aiki da ya sabawa dokoki da dama na Majalisar Dinkin Duniya, na zama wani abu da ke ninkin baninki kan irin laifukan da kasar ke yi a idan majalisar, wacce a yanzu ma ke duba yadda za ta hukunta mahukuntan na birnin Pyongyong bayan gwajin da suka yi na makamin nukiliya a watan da ya gabata.

Tuni dai Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana bukatar ganin Koriya ta Arewa ta tsaida duk wani yunkuri da take yi da ka iya harzuka al'ummomin kasa da kasa.