Koriya Ta Arewa ta ce babu ja da baya a shirinta na nukiliya | Labarai | DW | 16.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya Ta Arewa ta ce babu ja da baya a shirinta na nukiliya

Kasar KTA ta ce ba zata shiga tattaunawa akan shirinta na nukiliya ba, muddin takunkumin Amirka ta sanya mata ya ci-gaba da aiki. Mataimakin shugaban KTA Kim Yong-nam ya fadawa taron kolin kasashe ´yan baruwanmu a birnin Havana na kasar Cuba cewa kasar sa na bukatar makaman nukiliya don kare kanta. Tun a cikin watan nuwamban bara KTA ta janye daga tattaunawar da ake yi tsakaninta da KTK, China, Japan, Rasha da kuma Amirka akan shirinta na nukiliya. Furucin na mista Kim ya yi kama da sanarwar da shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya yi, wanda ya fadawa mahalarta taron cewa gwamnatinsa zata gaggauta amfani da shirin samar da makamashin nukilkiya cikin lumana. Amirka da KTT na zargin Iran da KTA da tafiyar da shirin kera makaman nukiliya.