Koriya Ta Arewa ta amince da yarjejeniyar rufe tashoshin nukiliyar ta | Labarai | DW | 03.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya Ta Arewa ta amince da yarjejeniyar rufe tashoshin nukiliyar ta

Shugaban Amirka GWB yayi maraba da yarjejeniyar da aka cimma wadda a karkashin ta KTA zata rufe dukkan tashoshinta na nukiliya kafin karshen wannan shekara. A karshen mako aka tsara ka´idojin yarjejeniyar a gun wani taro na kasashen nan 6 da suka hada da China, KTK da TA, Japan, Rasha da kuma Amirka a birnin Beijing. Idan dukkan kasashen 6 suka amince da yarjejeniyar kuma KTA ta aiwatar da ita to wannan yarjejeniya zata wani gagarumin ci-gaba da burin Amirka na shawo kan KTA ta yi watsi da shirin ta na nukiliya. Za´a saka ma kasar da jerin taimakon tattalin arziki.