1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Koriya ta Arewa ta ƙaddamar da gwajin makamin nukiliya

Gwamnatin Jamus ta yi tir da gwajin nukiliyar da Koriya ta Arewa ta yi a yau Litinin.

default

Tashar gwajin makamin nukiliya a birnin Pyongyang

Tun a cikin watan jiya na Aprilu ne dai, Koriya ta Arewan ta yi barazanar farfaɗo da ayyukanta na makamin nukiliya, kuma ta yi hakan ne a matsayin mai da martani na sukan da aka yi wa matakinta na harba roka da ta yi a watan da ya gabata. Lokacin da ta ce ta harba rokar ne domin aika wa da tauraron ɗan Adam zuwa sararin samaniya.

Dama tun a watan Oktobar shekara ta 2006, Koriya ta Arewa ta girgiza duniya ta hanyar gwajin da ta yi na makamin nukiliya ta ƙarƙashin ƙasa. Yanzu kuma sai ga shi a yau mahukunta a koriya ta arewan sun kara tabbatarwa da duniya cewa, sun sake yin gwajin wani makamin nukiliyar, inda suka bayyana sanrawar cewa, a yau 25 ga watan Mayu, sun sake yin gwajin wani makamin nukiliyar cikin nasara. A cewar su wannan makami wani abin buƙata ne ga masana ilimin kimiyyarsu da injiniyoyinsu domin kara inganta harkokin tsaronsu.

Hukumar Nazarin albarkatun ƙasar Koriya ta Kudu ta tabbatar da aukuwar wannan gwaji, inda ta ce ta gano wani yanayi kamar na girgizar ƙasa, da ke nuna cewa an yi gwajin makamin nukiliyar.

Baya ga gwamnatin Jamus, Shugabannin duniya da dama sun fito

Jens Plötner

Jens Ploetner, Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus

fili sun yi tir da wannan gwaji da Koriya ta Arewa ta yi. Jens Ploetner, shi ne kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus, kuma an jiyo shi yana cewa gwamnatin Jamus ta yi tur da wannan gwajin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi da kakkausar murya. Ya ce a ra'ayin Jamus wannan gwaji ya saɓa ƙa'idar Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma wannan gwaji barazana ce ga tsaron yankin. Ya ƙara da cewa Jamus na kira ga Koriya ta Arewa da ta ƙauracewa irin wannan takalar faɗa da take yi.

Jens Ploetner ya ce Jamus na fatan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin duniya zai yi zama na musamman akan wannan lamari, tare da fitar da wani ƙuduri tabbatacce. A cewarsa Jamus na goyon bayan duk wani mataki da za a ɗauka wanda zai kawo zaman lafiya a wannan yanki. Kafafen yaɗa labaran ƙasar Koriya ta Arewan sun tabbatar da cewa, wannan gwajin nukiliyar da aka yi, ya nunnunka wanda aka yi a shekara ta 2006 ƙarfi nesa ba kusa ba.

Koriya ta rewa dai ta janye daga tattaunawar da ake yi da ita game da kawo ƙarshen sarrafa makamin nukiliya ne, tun bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya tai Allah wadai da gwajin rokar da ta yi da sunan harba tauraron ɗan Adam, wanda kuma ƙasashen yamma suke kallo a matsayin fakewa da guzuma domin a harbi karsana. Wato fakewa da tauraron ɗan Adam domin harba makami mai linzami.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Zainab Muhammed Abubakar