Koriya ta Arewa na yin tunanin watsi da shirinta na nukiliya | Labarai | DW | 08.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa na yin tunanin watsi da shirinta na nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi gargaɗin cewar ƙasarsa ba za ta yi amfani da makaman nukiliya ba a kan wata ƙasa sai fa idan a tsokaneta a kan yancinta.

Kim Jong Um wanda ke yin magama a wajen babban taro na jam'iyyar da ke yin mulki ta ma'aikata watau PTC wanda rabon da a yi irinsa tun a shekara ta 1980. Ya ce ƙasarsa za ta taimaka wajen hana yaɗuwar makaman nukiliya a duniya, tare da neman sake daidaita hulɗa da Amirka da kuma Koriya ta Kudu.

A baya dai Koriya ta Arewa ta shan yi barazanar cewar za ta kai wa Amirka da Koriya ta Kudu hare-hare na makaman Nukiliya, tare kuma da ƙaddamar gwaje