Korea ta Arewa ta amincewa komawa tebrin shawara | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Korea ta Arewa ta amincewa komawa tebrin shawara

Korea ta Arewa ta ce, a shire ta ke, ta koma tebrin shawara a game da rikicin na, makaman nuklea.

Idan dai ba a manta ba, a farkon watan da mu ke ciki, hukumomin Pyong Yang, su ka yi gwajin wannan makamai , matakin da ya jawo musu Allah wadai, daga ƙasashen turai, da Amurika.

Bayan cece-kuce mai tarin yawa akan wannan batu, a ƙarshe, Korea ta Arewa, ta lashe amen ta.

Amurika da Britania, sun yi lalle marhabin da wannan saban mataki, sun kuma yabawa ƙasar Sin, a game da rawar da ta taka, wajen ciwon kan Pyong-Yang.

Cemma,jim kaɗan ,bayan da Korea ta Arewa, ta yi gwajin makamin nuklear, mataimakin sakataran harakokin wajen Amurika, Christopher Hill, ya ce sai ta yi cizon yatsa.