Kongo: Alfaharin kasancewa Zabiya | Duka rahotanni | DW | 31.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kongo: Alfaharin kasancewa Zabiya

Zabiya a kasar Kwango sun tashi tsaye don kare kansu, bisa nuna musu wariya da ake yi, don haka kungiyar Zabiya ta shiya bikin karfafa gwiwar wadanda matsalar ta shafa

"Fièrement Ndundu"- Shi ne bikinsu na farko na alfahari da kasancewarsa Zabiya Hakan ya zama tamkawa wani dan karamin juyin juya hali ne. Bikin na tsawon kwanaki uku a Kinshasa babban birnin kasar Kwango, an shirya shi ne bisa samun karuwar karbuwa daga jama'a. A jawabai mahalartan na son yin musayar ilimi. Soyayya da amincewa daga jama'a dai abu ne da tun ranar farkon bude bikin aka samu, inda cikin mahalata taron ba wai masu fama da larurarl Zabiya ne kawai suka hallara ba.