1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kone-konen motoci a kasar Faransa

November 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvLn

Ministan cikin gida na Fransa Nikola Sarkozy, ya kiri gwamnonin jihohin Fransa dake fama, da kone konen motoci, da su dauki matakan korar duk wanda suka samu, da hannu a cikin wannan danyan aiki, zuwa kasar sa ta assuli, ko da kuwa mutumen na da cikkakun takardun zama Fransa.

Mafi yawan masu kone konen matasa ne, yaku bayi, yan assulin kasashen Afrika, da sauran yankuna larabawa.

Ya zuwa yanzu, kimanin motoci dubu 5 ne, masu zanga zangar su ka kona, tare da gidaje , shaguna da makarantu.

Gwamnatin kasar Fransa ta kafa dokar ta ba ce, to saidai wannan doka, ba ta yi wani anfani ba, idan akayi la´akari da yawan motocin da a ka kona a daren jiya.

A dangane da wannan rikici, sakataran kungiyar kasashe musulmi ta dunia, Ekmeldin Ihsanoglu, ya yi kira ga musulmin kasar Fransa, da su kasance masu biyyaya, da bin doka da oda, su kuma kauracewa dukan irin wannan ayyuka, da su ka sabawa dokoki da tarbiyar musulunci.

A daya gefen, Ekemeldin ya gayaci gwamnatin Fransa, da ta dauki matakan kyawttata rayuwar mazamna kasar ta, ba tare da nuna wariya ba.