Kondalisa Rice ta kai ziyara a Afganistan | Siyasa | DW | 12.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kondalisa Rice ta kai ziyara a Afganistan

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Kondalisa Rice ta kai ziyara a Afganistan, jim kadan bayan harba rokoki a yankuna daban daban na kasar.

Rice

Rice

Wasu tagwayen haren haren bama bamai, sun hadassa mutuwar mutane 11, a sahiyar yau laraba, a kudancin Afganistan, da ke fama da yake yake.

Harin farko ya wakana a kusa da Kandahar, inda ya hallaka mutane 5, membobin wata kungiyar bada agaji mai zaman kanta, Afhgan Healft Services, a yayin da mutane 3 su ka ji mummunan raunuka.

Hari na 2 ya wanzu a jihar Uruzgan, wanda shi kuwa ya jawo mutuwar yan sanda 6, inji gwamnan jihar, Jean mohamed Khan.

A Kabul, babban birnin kasar yan takife, su harba rokoki da su ka raunana jami´an kulla da tsaro a gidan jikadan kasar Kanada a Afganistan.

Jim kadan kuma, wasu karin rokoki su ka fada gap ga sansanin sojojin kasa da kasa, na ISAf, da ke kewayen birnin Kabul.

Kakakin rundunar sojojin ya sanar manema labarai cewa, basu da cikkakar masaniya, ko wannan hare hare , na da niyar abkawa sassanin.

Harbe-harben, sun wakana sa´o´i kadan, kamin saukar sakatariyar harokokin wajen Amurika, Kondolisa Rice a birnin Kabul.

Rice, ta fara rangadin kwanaki 3, a yankunan tsakiyar Asia,a ranar litinin.

A ganawar da ta yi da shugaban kasar Afganistan, Hamid Karzai, sun tantana a kan batutuwa daban daban ,da su ka shafi hulddin diplomatia da kwanciyar hankali.

Bayan zaben yan majalisun dokoki na 18 ga watan da ya gabata, kasar Afganistan ta buda wani sabon shafi a cikin tarihin ta, inji Kondolisa Rice a kashen ganawar.

Mahimman batutuwan da magabatan 2, su ka zanta a kai, sun hada da noman ganyi wiwi, wanda akan sa, Afganistan , ta yi kaurin suna a dunia.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika ta halarci taron majalisar ministocin Afganistan, inda su ka cenza miyau a kan batun noman wiwi, da Afganistan ke sahun gaba, a jerin kasashe masu noma, wannan taba.

Rice ta yi, kira ga hukumomin kasar, da su kara matsa kaimi ,wajen yaki da wannan mumunar sana´a.

A daya gefen kuma, sun yi masanyar ra´ayoyi, a kan batun sojojin kungiyar tsaro ta NATO, da ke kasar domin, tabatar da zaman lahia.

Rice ta shaidawa Hamid Karzai, niyar Amurika ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin Afganistan, har lokacin da kasar ta zauna daram bisa dawwamamar turbar zaman lahia.

Kungiyar tsaro ta NATO na jagorantar rundunar ISAF, da ta kunshi dakaru 8500 daga kasashe kimanin 30 na dunia.

Akwai kuma alamun kungiyar, za ta kara yawan sojojin nan da yan watani masu zuwa, a yankuna da ke fama da tashe tashen hankulla.

Bayan rundunar Isaf, Amurika na da sojoji a kalla dubu 20 ,a kasar Afganistan da ta aika tun bayan hambaren mulkin yan taliban.

A karshen ziyara a birnin Kabul,Kondolisa Rice, ta yi gasuwa da jinjinna damtse, ga membobin tawagar kwantar da tarozoma, da kuma jami´an opishin jikadancin Amurika a Afganistan.

A dazun nan ne Kondolisa Rice ta kamala ziyara a Afganistan, nan gaba a yau zata issa Pakistan, domin gani da ido, illolin da girgizar kasa ta hadasa.

Rice zata tanttana da shugaban kasar, Pervez Musharaf da kuma Praminista Shaukat Aziz, a game da billa´in da ya sauka a kasar Pakistan ranar assabar da ta wuce.

Alkalummamn wucun gadi, da a ka bayyna jiya, sun sannar cewa, mutane dubu 23 ne, su ka rasa rayuka a wannan masifa da kuma dubu 51, da su ji raunuka,a yayin da a kalla mutane million 2 da rabi, su ka rassa matsugunai.

Kondolisa Rice, ta yi alkawarin tantanawa da shuwagabanin kasashen turai, a sati mai zuwa, domin gama karfi da Amurika, na samar da taimako mai kwari, ga mutanen da billa´in ya rutsa da su.

 • Kwanan wata 12.10.2005
 • Mawallafi yahouza sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvYs
 • Kwanan wata 12.10.2005
 • Mawallafi yahouza sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvYs