Komitin sulhu zai kara waadin aikinsa a yammacin sahara | Labarai | DW | 01.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu zai kara waadin aikinsa a yammacin sahara

Komitin sulhu ya kara waadin dakarun wanzar da zaman lafiya na majaliar dake yammacin sahara.Cikin kuduri daya dauka a jiya laraba komitin sulhun yayi kira ga samarda kafar tattaunawa tsakanin gwamnatin Morocco da yan tawayrn Polisario domin kawo karshen rikici na shekara da shekaru dake tsakaninsu.Komitin ya kara waadin jamian su 225 ne zuwa ranar 30 ga watan afrilu na shekara mai zuwa,yana mai kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da tattaunawa ba tare da kafa wasu kaidoji ba.Gwamnatin Morocco dai tuni ta bada tayin baiwa yammacin sahara yan cin gashin kai karkashin mulkin Morocco.Kungiyar ta Polisario a nata bangare tana neman a jefa kuriar raba gardama akan bada yancin kai baki daya ga jamaar saharawi da suke zaune a cikin hamada na arewa maso yammacin Afrika.Bangarorin biyu dai sun amince su gana gaba da gaba karo na farko cikin shekaru 7 bayan da komitin sulhu ya amince da wani kuduri da yayi kira ga bangarorin biyu da su zauna kann teburi guda domin sanasanta tsakaninsu.Inda suka gana sau biyu wanda sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon yace basu tabuka wani abin azo a gani ba.