Komitin sulhu zai aika tawaga zuwa taron AU | Labarai | DW | 10.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu zai aika tawaga zuwa taron AU

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai aike da wata tawagarsa zuwa wani babban taro tsakanin kungiyar AU da Sudan wadda zaa gudanar ranar litinin tare da sakon cewa har yanzu tana goyon bayan MDD ta karbi aiyukan wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur.

Taron na AU da zaa gudanar a babban birnin Habasha zai tattauna makomar dakaru 7,000 na AU wadanda waadin aikinsu zai kare a karshen watan disamba.

Shugaban komitin mai ci yanzu jakadan kasar Peru a Majalisar Jorge Voto-Barnales yace duk da kin amincewar Sudan,tawagar mutum 8 ta komitin zata bukaci kaddamar da kudirin da zai bata damar karbar aiyukan zaman lafiya a yankin Darfur.