1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin sulhu yayi Allah wadai da tawaye a Chadi

Hauwa Abubakar AjejeApril 14, 2006

Komitin sulhu yayi kira ga Chadi da Sudan da kada su ci gaba da kawo rudani tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/Bu0b
Shugaba Idris Deby
Shugaba Idris DebyHoto: AP

Tchadi dai yanzu haka tana zargin Sudan da haddasa rikici da yan tawaye suka kaddamar akan shugaba Idris Deby Itno,kodayake Sudan ta karyata wannan zargi.

Bisa shawara da kasar Kongo wadda ke rike da shugabancin Kungiyar Taraiyar Afrika yanzu ta bayar,komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya,ya tattauna halin da ake ciki a Chadi,wadda take makwabciya ga yankin Darfur na kasar Sudan da yaki yayi kaca kaca da shi.

Wakilin kasar Sin wadda ke shugabancin komitin sulhu a wannan wata,Wang Guangya,ya baiyana cewa,membobin komitin suna Allah wadai da duk wani yunkuri na karbar mulki da karfi,sun kuma yi kira ga yan tawayen da su kawo karshen tashe tashen hankula tare da shiga harkokin demokradiya na kasar.

Hakazalika komitin sulhun ya bukaci gwamnatocin kasashen Chadi da Sudan da su bi kaidojin yarjejeniyar 8 ga watan Fabrairu wanda a karkashinta suka amince ba zasu bada mafaka ga yan tawaye dake bakin iyakokinsu ba,ba zasu kuma yi fada tsakaninsu ba.

A halin da ake ciki dai,sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya,Kofi Annan,ya nuna damuwarsa game da halin tsaro da yake kara tabarbarewa a kasar ta Chadi,inda yayi Allah wadai da kakkuasar murya rikici na baya bayan nan da yan tawayen suka tayar a kasar,yace ya kamata masu adawa su bi hanyoyin siyasa wajen sasanta banbance banbance dake tsakaninsu.

A dai jiya alhamis ne kasar chadi tayi ikrarin tarwatsa yan tawayen da suke kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Idris Deby daga babban birnin kasar N’djamena,ta kuma zargi Sudan da wannan yunkuri na kifar da gwamnatinta.

Jakadan kasar Faransa a Majalisar Dinkin Duniya dai,wanda kasarsa ta aike da Karin sojoji 150 akan 1,200 da take da su a Chadi,Jean-Marc de La Sabliere,yace,a gaskiya ana fuskantar yunkurin juyin mulki da karfin tuwo,wanda ba zai taba samun karbuwa ba.

Yace abinda yake faruwa a Chadi yana da alaka kai tsaye da abinda ke faruwa a yankin Darfur,inda yace wadannan yan tawaye daga Darfur suke kuma ci gaba ne na hare hare da suka gudana a watannin Maris da Disamban bara.

Jakadan na Faransa,yayi gargadin cewa,fada a yanzu,yana iya shafan zaman lafiyar yankin tsakiyar Afrika gabaki daya,inda yayi nuni da cewa,yan tawayen na Chadi sun ratsa ne ta jamhuriyar tsakiyar Afrika daga Darfur kafin shiga kasar ta Chadi

De La Sabliere,yace shugaban kasar Kongo Denis Sassou-Nguesso da Kofi Annan zasu tattauna wannan batu,hakazalika nan bada jimawa ba komitin tsaro na Kungiyar Taraiyar Afrika zai gana akan wannan batu.