Komitin Sulhu yayi Allah wadai da hari kan tawagarsa a Darfur | Labarai | DW | 12.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin Sulhu yayi Allah wadai da hari kan tawagarsa a Darfur

Komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fito da wata sanarwar haɗin gwiwa wadda ta yi Allah wadai da wani hari da aka kai kan tawagarta a yankin Darfur ƙasar Sudan a farkon wannan mako. Jami’an Sudan sun tabbatar da cewa dakarunsu sun buɗe wuta kan tawagar inda suka lalata ababen hawa guda biyu tare da raunata wani direba ɗan Sudan. Sanarwar ta kuma baiyana cewa komitin sulhun a shirye yake ya ɗauki mataki kan duk wani wanda zai kawo cikas ga shirin zaman lafiya ko aiyukan agaji tare da tura dakarun Majalisar da na AU zuwa Darfur.