Komitin sulhu yana duba irin takunkumi da zai lakabawa Koriya ta arewa | Labarai | DW | 10.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu yana duba irin takunkumi da zai lakabawa Koriya ta arewa

Komitin sulhu na majalisar dinkin duniya yana duba takunkumi iri daban daban da zai iya lakabawa Koriya ta arewa bayan Allah wadai da gwajin nukiliya da tayi ikrarin ta gudanar a jiya litinin.

Kasar amurka dai ta bada umurnin binciken dukkan jiragen daukar kaya zuwa koriya ta arewa domin kamme makaman da aka haramta shiga kasar da su.

Shugaba Bush ya kuma gargadi koriyan da kada ta fitar da makamanta ko abinda yayi kama da haha zuwa wasu kasashe ko kuma kungiyoyin yan taadda.

Nan gaba a yau ne komitin sulhu zai sake ganawa,kasar Burtaniya kuma tace mai yiwuwa ne aka lakabawa koriyan takunkumi cikin wannan mako.

Rasaha da Sin wadanda wadanda suke dari dari da batun takunkumin sunyi kira ga Koriya ta arewa data koma teburin tattaunawa na kasashe 6.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter-Steinmeier ya roki Koriyan da kada ta sake wani gwajin.