1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin sulhu ya koma tattaunawa akan Iran

March 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4B

Membobin komitin sulhu na MDD a yau suna ci gaba da kokarin nemo bakin zaren warware kiki kaka game da shirin nukiliya na kasar Iran,bayan kasashen Burtaniya da Faransa sun kira da da dakatar da tattaunawar saboda kasa samun cimma yarjejeniya musamman saboda dagewar kasashen Rasha da Sin akan yadda zaa bullowa alamarin.

Yanzu haka sun shirya komawa teburin tattaunawa a yau laraba domin fito da sanarawa ta bai daya.

Kasar Amurka dai tace har yanzu tana da imanin cewa,komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai iya cimma yarjejeniya cikin yan kwanaki masu zuwa na bukatar kasar Iran ta dakatar da sarrafa sinadaren yuraniyum.

Jakadan kasar Amurka a hukumar kula da kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa,Gregory Schulte,ya fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa,ya tabbata cewa sanarwar da komitin sulhun zai fito da ita,zata bukaci Iran din data kaddamar da dukkanin kaidojin da hukumar da shimfida mata,game da shirnita na nukiliya da ake ganin na kera makaman kare dangi ne.