Komitin sulhu ya kira taron gaggawa kan kasar Somalia | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya kira taron gaggawa kan kasar Somalia

Komitin sulhu na MDD ya kira wani taron gaggawa a yau game da rikicin kasar Somalia,bayan mako guda na fada tsakanin magoya bayan kotunan musulunci da dakarun gwamnatin rikon kwarya tare da goyn bayan dakarun Habasha.

Komitin sulhun mai membobi 15 zai fara taron ne nan gaba a yau din nan inda wakilin musamman na Kofi Annan,Francois Lonseny zai sanarwa da komitin game da halinda ake ciki a kasar ta Somalia.

Jakadan kasar Qatar ne a MDD Nassir Abdulaziz Al-Nassir shugaban komitin na watan disamba,ya bukaci gudanar da wannan taro cikin gaggawa,bayanda firaministan Ethiopia Meles Zenawi yace dakarunsa sun kashe mayakan islama kusan 1,000.