1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

komitin sulhu ya kakabawa jamian sudan 4 takunkumi

April 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6k

Gwamnatin Sudan tayi Alölah wadan kudurin da komitin sulhun mdd ya dauka na kakabawa jamian kasar guda 4 takunkumi ,adangane zargi da ake musu na hannu a zubar da jini da take hakkin jamaa a lardin Darfur,batu da sukace bazai a lokacin daya dace ba.kAkakin maaikatar harkokin wajen na Sudan Jamal Ibrahim ,yace hakan na iya durkusar da kokarin sasantawa da kungiyar Au keyi ,na warware wannan rikici daya bar mutane dubu 300 mace,ayayinda sama da million 2 suka tafi gudun hijira.Yace a yanzu haka dai a kusan warware rikicin na Dafur a birnin Abuja,kuma abunda ake bukata kadai shine goyon baya,amma ba amfani da wasu hanyoyi na hukunci ba.Komitin suhun dai a jiya ne ya amince da kakabawa wadannan jamiai takunkumi ta hanyar kuria,amm Rasha da Sin bayu halarci zaman ba.Akan hakane jakadan Amurka a MDD John Bolton yace wannan kuduri da komitin sulhu ya zartar,na tabbatar dacewa an dauki tsauraran matakai na tabbatar da zaman lafiya a darfur,wanda kuma bazai shafi tattaunawar Abuja ba……..Oton…

Mutane 4 da aka kakabawa takunkumin tafiya dana tattali dai sun hadar da Major General Mohammed Elhassan,dake jagorantar rundunar dakarun yammacin kasar,da Adam Yacub Shant,commandan sla,sai sheikh Hilal dake Arewacin darfur da kuma Gabril Abdul kareem Badri,comman mayakan dake marawa gwamnatin khartum baya.