1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu ya kaɗa ƙuri´ar share fage za zaɓen saban Sakatare Jannar na UN

July 25, 2006
https://p.dw.com/p/BupI

A shirye shiryen cenji Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia, komitin sulhu ya yi zagayen farko, na zaɓen share fage, tsakanin jerin yan takarkara guda 4, dukan su na nahiyar Asia.

A ƙarshen shekara da mu ke ciki ne,sakatare Jannar mai ci yanzu Koffi Annan, zai kai ƙarshen wa´adin mulkin sa, na jagorancin Majalisar Ɗinkin Dunia.

Ya zuwa yanzu, yan takara da su ka bayyana shawar hawan wannan kujera mai daraja, sun haɗa da ministan harakokin wajen Korea ta Kudu Ban Ki-Moon, da wani ƙurraren jami´in diplomatia na ƙasar Sri-Lanka, Jayantha Dhanapala,, da mataimakin Praministan Thailand Surakiart Sthiratai, sai kuma mataimakin shuguban hukumar sadarwa, ta Majalisar Ɗinkin Dunia Shashi Tharror na ƙasar India.

ƙasashen 15 membobin komitin sulhu na Mjajalisar ɗinkin Dunia sun kada ƙuri´ar share fage a kan wannan takara guda 4, saidai ba a bayyana sakamakon zaben ba. Wani jami´in diploamtia a Majalisar Dinkin Dunia ya sanar cewa, har yanzu masu buƙatar maye wannan kujera na da damar ajje takara.