Komitin sulhu ya gana akan rikicin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 10.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya gana akan rikicin gabas ta tsakiya

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gana jiya a birnin New York game da tashe tashen hankula dake ci gaba a yankin gabas ta tsakiya.

Kasashen larabawa dai suna kira da gaggauta tsagaita wuta a Gaza,wadda suka bukaci dakaru karkashin sa ido na Majalisar su kaddamar da shi.

Wakilin Palasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya zargi Israila da aikata laifukan yaki a yankin yana mai cewa ya kamata a kama wadanda suka haddasa wannan karkashin dokoki na kasa da kasa.