komitin sulhu ya fadada waadin sojin mdd a Golan | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

komitin sulhu ya fadada waadin sojin mdd a Golan

Komitin Sulhun MDD ya bada umurnin fadada waadin dakarun kulawa na majalisar akan tsaunukan Golan,inda ayarin dakarun suka kasance domin kasancewar masu shiga tsakanin Dakarun izraela dana syria na tsawon shekaru 32, da tsawon karin watannin shida.A halin da ake ciki yanzu dai a rahotansa na karshe gabanni sauka da mukaminsa na sakatare general na mdd a ranar 31 ga watan Disamba,Kofi Annan ya fadawa komitin sulhun cewa bazaa samu zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba,har sai izraela ta mikawa Syria tsaunukan na Golan.