Komitin sulhu ya amince a kawo Iran gabansa | Labarai | DW | 31.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya amince a kawo Iran gabansa

Kasar Amurka da sauran membobin komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun amince kaiwa Iran gaban komitin sulhun,game da batunta na nukiliya.

Kasashen Sin da Rasha wadanda kawayen Iran ne sun sanya hannu akan sanarwar da ta yi kira ga hukumar kare yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa,data mika batun gaban komitin domin duba yiwuwar lakaba mata takunkumi ko daukar wani mataki na ladabtar da ita.

Sai dai kasashen komitin sun amince dakatar da batun har sai watan maris bayan hukumar ta mika rahotonta game da aiyukan Iran na nukiliya.

Komitin sulhun ya kuma amince cewa hukumar zata bada bayanan shawarwari da ta yanke akan matakan daya kamata Iran ta bi,game da wannan batu.

Kodayake ba a tabbatar da ko sanya hannu da kawayen Iran sukayi akan wannan sanarwa,zasu amince da lakabawa Iran takunkumi ba.