Komitin sulhu ya ƙara ƙarfin mulki ga Charles Konnan Bany | Labarai | DW | 02.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya ƙara ƙarfin mulki ga Charles Konnan Bany

Shugaban ƙasar Cote d´Ivoire, Lauran Bagbo, ya gabatar da jawabi, inda ya nuna gamsuwa ga ƙudurin komitin sulhu na MDD, wanda ya amince, da bashi damar ci gaba da jagorancin ƙasar, har ranar 31 ga watan okober na shekara ta 2007, tare kuma da ƙarfafa mulkin praministan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Bany.

Komitin, ya ɗauki wannan mataki, domin baiwa Konnan Banny, damar shirya zaɓɓuɓuka daban-daban, a ƙasar nan da shekara ɗaya.

Itama Ƙasar France, da ta gabatar da wannan ƙuduri, ta bayyana gamsuwa, ga saban matakin da Majalisar Ɗinkin Dunia ta ɗauka, a kan Cote D´Ivoire.

Kafofin sadarwa masu bada goyan baya ga shugaban Cote D´Ivoire, sun fassara ƙudurin da matsayin yunkurin juyin muklki, duk da cewar, a ganin su France, ba ta cimma baki ɗaya, burin da ta sa gaba ba, na ƙwace kwata-kwata, harakokin mulki, daga shugaba Bagbo.