1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya yi kashedi ga Ethiopia da Eritrea

Yahouza SadissouNovember 24, 2005

KomitinSulhu na majalisar Dinkin Dunia ya gayyaci kasashen Ethiopia da Eritrea da su kwance damara yaki

https://p.dw.com/p/Bu3x

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya yi barazanar daukar matakan saka takunkumi ga kasashen Ethiopia da Erytrea muddun ba su fasa shirye shiryen da su ke ba na kai wa juna hari.

Membobin komiti su 15 baki daya,sun cimma daidaito a game da wajibcin daukar matakan ladabtarwa, ga wannan kasashe,da zaran su ka yi kunen uwar shegu, ga bukatar da Komitin Sulhu ya gabatar masu.

A daya gefen, komitin yayi kanda ga hukumomin Erytera da su janye dokar da su ka dauka, ta hana wa jiragen sama, masu durra angullu na rundunar shiga tsakani ta Majalisar Dinia, shawagani a sararin samaniyar kasar.

Wannan mataki da hukumomin Asmara su ka dauka a watan da ya gabata ya kawo matukar cikas, ga ayukan tabbatar da zaman lahia a wannan yanki da yayi fama da yake yake.

A hukuncin da ya yanke a yammacin jiya komitin sulhu ya bayyana wa kasashe 2, cewa duk wadda ta burjinewa umurnin, babu makawa, matakin karshe, shine na saka mata takunkumin karya tattalin arziki, da kuma maiyar da ita saniyar ware a fagen diploamtia na dunia.

Kazalika komitin sulhu ya yi kira ga Ethiopia da ta amince cikin gaggawa da iyakar da a ka shata, tsakanin ta da Erytrea.

Idan ba a manta ba, a shekara ta 2000 kasashen su ka rataba hannu a kan yarjeneniyar zaman lahia bayan shekaru 2, na yaki tsakani su, da ya hasada mutuwar mutane kimanin dubu dari 8.

Sakamakon wannan yarjejeniyar, ya tanadi girka komiti da zai shata iya tsakanin kasashen 2.

Komitin ya kammala ayyukan sa tun shekara ta 2002, to saidai har yantzu shata iyar ya faskara.

Ethiopia ta bayyana kin amincewa da aikin da komitin ya gabatar.

A game da haka, Erythrea ta yi watsi itama da dokokin sulhun da aka cimma a sakamakon haka sai ciwo ya koma danye.

A baya bayan nan tawagar majalisar Dinkin Dunia a yankin ta buga rahotani masu tayar da hankali a kan shirye shiyren kasashe 2 na komawa fagen daga.

Sanarwar komitin sulhu ta jiya ta gayyaci gwamnatocin Ethiopia da na Erytrea, da su maiyar da dakarun su a gurabensu, na daidai ranar 16 ga watan disember na shekara ta 2004, wanda shine matsayin da su ka nuna, na bukatar cimma zaman lahia.

A karshe membobin Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia sun gayyaci sakate jannar Koffi Annan, ya bi diddikin al´amarin ya kuma gabatar da rahoto a kai nan da kwanaki 40 masu zuwa.

A karshen wannan wa´adin komiti sulhu za shi sake saban zama domin bitar nassarori da kuma matsalolin da a ka cimma tare ,da matakan da ya kamata a dauka.