1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin sulhu na ci gaba da tattauna batun takunkumi akan Iran

December 21, 2006
https://p.dw.com/p/BuWs

Komitin sulhu na MDD yana tattauna wani kudiri da aka sabunta game da takunkumi da zaa dorawa kasar Iran kann shirinta na nukiliya.

Kasashen Burtaniya,Faransa da Jamus sunyi kokarin kwantar hankalin Rasha da Sin game da takunkumin zirga zirga kann shugabanin siyasa da yan kasuwa tare da wasu kuma wasu mutane 12 dake da hannu cikin shirin nukiliya na Iran.

Amurka da kasashen turai suna dai fatar ganin an samu kuriar amincewa da wannan kuduri a gobe jumaa.

Kudirin dai zai haramta shige da fice na kayaiyaki da fasahohi da suka shfai inganta sinadaren uranyium.

Iran dai tayi barazanar maida martani muddin dai an amince da wannan kuduri.