1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komitin sulhu akan Iran

September 28, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9z

Manyan kasashen duniya masu fada aji sun cimma matsaya guda adanagne da jinkirta daukan matakai na tsaurarawa Iran takunkumi.A taron da suka gudanar a birnin New York din Amurka,kkasashen dake zaunannun kujera a komitin sulhun mdd ,hade da jamus,da kugiyar tarayyar turai ,sun amince da bada karin lokaci zuwa watan Nuwamba ,dangane da rahoton hukumar kula da harkokin nuclear ta majalisar, akarkashin jagorancin Mohammed El Baradei da jamiin kula da harkokin ketare na kungiyar Eu Javier Solana.A bayyana take a wajen wannan taron dai cewar,kasashen Sin da Rasha sun bukaci a bawa hukumar nuclearn karin lokaci na gudanar da bincikenta.ayayinda kasashen Amurka da Faransa da Britania da Jamus ,sukayi kokarin ganin cewa an kakabawa Iran wani zagayen takunkumi,saboda cigaba da bunkasa sinadran uranium dinta,wanda kasashen yammacin ke ganin cewa zata iya sarrafa makaman nuclear dashi.