1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

komawa tattaunawar kafa gwamnati a Iraqi

March 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4A

A yau shugabannin siyasa na kasar Iraq zasu koma tattaunawar kafa sabuwar gwamnati,yayinda yan shia dake cikin majalisa suka ce basu da shirin watsi da shirinsu na sake mika Ibrahim al Jaafari a matsayin Firaminista.

A ranar lahadi aka dakatar da tattaunawar wadda jakadan Amurka Zalmay Khalidzad ya nema ayi,saboda bukukuwan yan shia da Qurdawa.

Khalizad yana mai matsawa yan siyasa na Iraqi da su kawo karshen kiki kaka da aka samu game da ci gaba da shugabancin al jaafari,wanda yan sunni da Qurdawa da kuma bangarorin masu sassucin raayi suke adawa da kakkausar murya.

Gamaiyar jamiyun shia dai tana da kujeru 130 cikin kujeru 275 na majalisar dokokin Iraqi.