Koma baya kan fitar Birtaniya daga EU | Siyasa | DW | 24.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Koma baya kan fitar Birtaniya daga EU

Kotun kolin kasar Birtaniya ta yanke hukuncin cewa kasar ba za ta iya fara amfani da kudirin dokar da ya tanadin hanyoyin da kasar da ke son ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai za ta bi, har sai majalisa ta bata dama.

Da gagarumin rinjaye ne dai kotun kolin ta yi watsi da karar da gwamnatin kasar ta daukaka kan batun na matakan kammala ficewar Birtaniyar daga Kungiyar Tarayyar Turai  wato EU, da al'ummar kasar suka kada kuri'ar amince wa. Da yake yanke hukuncin, babban Alkalin kotun kolin mai shari'a David Neuberger cewa ya yi.

"A yau da rinjayen alkalai takwas cikin shadaya, kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnati ba za ta iya fara amfani da kudirin doka ta 50 da ta yi tanadin hanyoyin da kasar da ke son ficewa daga kungiyar EU za ta bi ba, wato Article 50 har sai majalisar dokoki ta ba ta damar yin hakan da kuma bayyana hanyoyin da gwamnatin ya kamata ta bi yayin ficewar. Dalilan da alkalan suka bayar kuwa sune: sashi na biyu na kudirin doka ta shekara ta 1972 ya bayyana cewa, a duk lokacin da kungiyar EU ta yi wata sabuwar doka, wadannan sababbin dokoki sun zama wani bangare na dokokin Birtaniya. Kundin dokokin na 1972 ya sanya dokokin Tarayyar Turai sun zama wani bangare na dokokin Birtaniya, har sai majalisar dokoki ta yanke hukunci a kansu. A dangane da haka in Birtaniya ta fice daga EU, za a cire wani bangare na dokokin Birtaniya ke nan, kana a sauya wasu damarmaki da 'yan Birtaniya ke da su. Saboda wannan dalili gwamnati ba za ta iya amfani da kudirin dokar na Article 50 ba, ba tare da majalisar dokoki ta bata wannan dama ba." 

Sai dai ga dukkan alamu wannan hukunci bai yi wa bangaren gwamnatin Birtaniyan dadi ba domin kuwa a zantawarsa da manema labarai, babban mai shigar da kara na gwamnati Jeremy Wright cewa ya yi:

"Tabbas gwamnati ba ta ji dadin wannan hukuncin ba, sai dai mun ji dadin cewa muna zaune a kasar da ya zama tilas kowa da kowa hatta gwamnati sai sun bi doka. Gwamnati za ta yi biyayya ga wannan hukuncin. Kotun ta bayyana karara cewa ba wai tana yanke hukunci kan Birtaniya ta fice ko kuma kada ta fice daga kungiyar EU bane, al'ummar Birtaniya sun riga sun zabi abin da suke so. Abin da ya rage yanzu shi ne aiwatar da abin da al'ummar suka zaba, wanda ya kasance batu na siyasa ba na shari'a ba. A dangane da haka sakatare mai kula da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai David Davis zai yi jawabi a gaban majalisar dokoki nan gaba kadan."

A nata bangaren jagorar masu karar Gina Miller nuna farin cikinta ta yi dangane da abin da ta kira amincewa da hukuncin, inda ta kara da cewa:

"Babu wani Firaminista ko gwamnati da zai tsammaci zai iya tsallake a kalubalance shi ko kuma ya tsallake hukunci, majalisar dokoki ce kawai ke da iko. Hukuncin na yau ya nunar karara cewa 'yan majalisun da muka zaba ne kadai za su iya yin abin da ya kamata wajen taimakon gwamnati ta cimma burinta na tattaunawa kan kammala ficewa daga kungiyar EU. Gaskiya ne cewa ficewar Birtaniya daga EU abu ne da al'umma suka amince da shi, amma sai dai tilas a girmama doka ba kawai abi son rai irin na siyasa ba." 

 

Sauti da bidiyo akan labarin