Kokarin yaki da cutar murar tsuntsaye a Nigeria | Labarai | DW | 01.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin yaki da cutar murar tsuntsaye a Nigeria

Bankin duniya ya amince da bawa Nigeria rancen dalar Amurka miliyan 50, don yaki da cutar nan ta murar tsuntsaye.

Sanarwar hakan data fito daga mahukuntan kasar a yau asabar, ta tabbatar da cewa za´ayi amfani da kudaden ne wajen daukar matakan rigakafi na hana cutar yaduwa a tsakanin tsuntsaye da dabbobi a hannu daya kuma daga jikin tsauntsayen izuwa jikin bil adama.

A waje daya kuma mahukuntan Amurka sunyi alkawarin bawa kasar ta Nigeria tallafin dala miliyan 25 don gudanar da wannan gagarumin aikin.

Kasar dai ta Nigeria idan an tuna ta kasance kasa ta farko a Africa data fuskanci bullar cutar murar tsuntsayen a watan fabarairun wannan shekara da muke ciki.