Kokarin warware rikicin Kosovo | Labarai | DW | 23.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin warware rikicin Kosovo

Jakadan Jamus Wolfgang Ischinger zai fara rangadin aikin na kwanaki biyu a Kosovo,domin tattaunawa da manyan jamian yankin Serbia daake fama da rikici.An dai nadashi a matsayin wakilin kungiyar tarayyar turai a tattaunawar dakie da nufin samar da makoma wa kosovo a siyasance,wadda ta hadar da wakilai daga Amurka da Rasha.Sakatare general na mdd Ban Ki Moon,ya bawa tawagar bangarorin uku watanni 4,na shawo kann sabanin dake tsakanin yan kabilar Albaniyawa masu rinjaye dake Belgrade da kosovo.Serbia dai tayi watsi da shirin mdd na bawa yankin Kosovo yancin kai,kuma Rasha tayi barazanar hawan kujerar naki a akomitin sulhu,domin hana yiwuwar hakan.A mako mai zuwa nedai akesaran gudanar da tattaunawar bangarori biyar adangane da makomar Kosovo,a birnin Vienna.