1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin Turai na dakile bakin haure

March 2, 2017

Shugaban hukumar gadin iyakokin gabar ruwan Turai FRONTEX ya sanar da kafa wani rashe da zai rinka saka ido don dafawa kokarin Turai da Afirka na shanyo kan matsalar kwararar bakin haure ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/2YWuh
Flüchtlinge in Melilla Polizei Grenzzschutz Grenzzaun Helikopter 06/2014
Hoto: Reuters/Jesus Blasco de Avellaneda

 

A Jamhuriyar Nijar shugaban hukumar gadin iyakoki da gabar ruwan kasashen Turai FRONTEX ne ya ambaci kafa wani rashe na hukumar da zai rinka saka ido don dafawa kokarin kasashen Turai da nahiyar Afirka shanyo kan matsalar kwarar bakin haure da ke bi ta barauniyar hanya don zuwa kasashen.

Wannan dai shi ne karonsa na farko da hukumar ta ambaci kaddamar da irinsa, a wata kasa daban da ke yammacin Afirka.

 
A yayin wani taron manema labarun da shugaban hukumar FRONTEX Fabrice Leggeri ya jagoranta a albarkacin wani taron kasa da kasa da ya hada nahiyar Afirka da Tarayyar Turai, game da matsalolin bakin haure da tsaro kan iyakokin bangarorin biyu ne dai, ya ambaci  kaddamar da tsarin a da ke zama irinsa na farko ga Afirka bayan amincewa da shawarwarinsa da hukumomin kolin kasashen Turai suka yi a baya.

Babban gurin da kafa wannan shashen zai sakawa gaba shi ne, na hada gwiwa da kasashen Afirka da Turai don samun cikakken bayyanai da kuma amfani da su wajen daukar matakai, tun daga tushe a wani yunkuri na kare dubban 'yan Afirka ga halaka ya'alla a hamadar sahara ko kuwa a teku idan sun tsallaka daga kasar Libya don zuwa Turai ta baraubniyar hanya,

Tsarin dai na hukumar FRONTEX zai kasance ne a Jamhuriyar Nijar wanda shugaban hukumar ya ce zabar Nijar a cikin sabuwar tafiyar na da mahimanci.

Lampedusa Triton Patrouillenschiff Viana do Castelo
Jami'in tsaron ruwa ta kan iyakaHoto: DW/B. Riegert


Fabrice Leggeri kenan ke cewar dalilin zabar Jamhuriyar Nijar shi ne Tarayyar Turai na da hulda ta kut da kut da kasar, kana sannu a hankali huldar da ke tsakanin kasashen na mu na cigaba da armashi. Ko baya ga wannan da akwai wasu hukumomin Turai ire-iren su EUCAP Sahel Nijar da ke aikin tsaro a kasar. To amma duk da hakan Nijar na a matsayin kasar da ake da damar hada karfi da karfe tsakanin kasashen domin ita daya ce hanya kana ita ce kuma damar da ke baiwa bakin haure kubuta daga balaguro marar tabbas a cewar da yawa da muka tattauna da su.