Kokarin tabbatar da zaman lafiya a Magadishu | Labarai | DW | 28.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin tabbatar da zaman lafiya a Magadishu

Rahotanni daga Somalia na nuni da cewa ako wane lokaci a nan gaba dakarun gwamnati tare da taimakon dakarun kasar Habasha, zasu karbi ragamar tafiyar da iko a birnin Magadishu.

Hakan kuwa ya biyo bayan janyewar dakarun kotunan Islama ne daga birnin. To amma kafin janyewar tasu, kafafen yada labarai sun rawaito su suna cewa ,sun yi hakan ne don kaucewa ci gaba da rikicin zubar da jini.

Ya zuwa yanzu dai an rawaito kakakin gwamnatin rikon kwarya na kasar na cewa tuni aka zartar da dokar ta baci, a wani yunkuri na ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a birnin na Magadishu.

Duk kuwa da cewa kwamitin sulhu na Mdd a zaman sa karo na biyu ya gaza cimma matakin kawo karshen wannan rikici na Somalia, Sakataren Mdd mai barin gado, Mr Kofi Anan hannun ka mai sanda yayi ga makotan kasashen na Somalia.

Barkewar wannan rikici dai ya samo asali ne mako daya ,daya gabata bayan Habasha taki janye dakarun sojin ta data jibge a Somalian, kamar yadda dakarun kotunan Islama suka bukata.