1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkuri na neman sulhu a Sudan ta Kudu

Yusuf Ibrahima Jargaba/ MABJuly 14, 2016

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya tura wakiliya ta musamman Sudan ta Kudu domin yin gargadi ga bangaren shugaban kasar da mataimakinsa da su gaggauta yin sulhu.

https://p.dw.com/p/1JOxh
Ban Ki-moon in Südsudan
Hoto: Reuters/J. Solomon

A lokacin da ta isa fadar shugaban kasa Salva Kiir a birnin Juba, wakiliyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ellen Margrthe Loj ta jaddada sakonsa na tabbatar da mutunta dokokin kasa da kuma 'yancin al'umma. Jami'ar ta kuma kara da cewa:

"Tabbas akwai bukatar mu samar da mafita a harkar siyasar Sudan ta kudu dan samar da zaman lafiyar da zai amfanin al'ummar kasar"

Wakiliyar ta Ban ki-moon ta kuma ci gaba da bayyana irin abubuwan da suka tattauna da mahukutan naSudan ta Kudu da ke fada da juna. Ta ce:

"Mun tattauna bukatar agajin gaugawa daga Majalisar Dinkin Duniya don tabbatar da ganin komai ya daidaita a kasar, wanda ya hada da bada taimakon jinkai ga yan´uwanmu don tabbatar da an kai daukin jinkan ga al'umma."

Südsudan Präsident Salva Kiir und Vizepräsident Riek Machar
Rieck Machar da Salva Kiir ba sa mutunta yarjejeniyar tsagaita wutaHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Rikicin Sudan ta Kudu ya ki cinyewa

Kalubalen da wannan kasa ta Sudan ta Kudu ke fuskanta na kashe-kashen al'umma ya sa Shugabanni da dama kan kai ziyara a kasar gami da yin tofin Allah tsine musamman a kan masu ruruta wutar rikicin. Babban Limamin majami'ar katolika da ke juba Paulino Lukudu Loro ya yi tir da wannan aika-aika a lokacin da ya isar fadar Shugaba Kiir..

Ya ce "Naje ne don in nuna matukar damuwar al'ummar wannan kasa ta Sudan ta Kudu musamman ma a birnin Juba kan mummunan abin da ya faru saboda abin ya munanan kwarai da gaske. Wannan aiki ne na shedanu.r"

Wannan rikicin ya ritsa da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 'yan asalin China. Saboda haka ne mahkuntan kasarsu suka dauki dakarun nasu da aka raunata zuwa Yuganda dan basu daukin gaugawa.

Südsudan Opposition Soldaten
'Yan tawaye ne ke fafatawa da sojojin gwamnatiHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Zhao Yali shi ne Jakadan kasar China a kasar Yuganda ya bayyana cewa: "An sanar damu cewa za´a kawo sojoji hudu a Yuganda. Saboda haka ne muka garzaya da abokan aiki na ofishin jakadancinmu zuwa filin jirgi domin dauko uku daga cikin dakarun wadanda suka samu raunuka"

Wannan fadan ya barke a Sudan ta Kudu lokacin da kasar ke gab da murnar cika shekaru biyar da samun 'yancin kai. Sudan ta Kudu dai ta sha fama da rikice-rikice tsakanin magoya bayan shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Rieck Machar.