Kokarin shawo kan rikicin yankin Darfur na Sudan | Labarai | DW | 26.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin shawo kan rikicin yankin Darfur na Sudan

Babban sakataren Mdd, Kofi Anan ya bukaci Mdd data dauki kwararan matakai na shawo kann rikice rikice da tashe tashen hankula dake faruwa a yankin Darfur na kasar Sudan.

A cewar Kofi Anan , a yanzu haka akwai matsalar karacin kudade da bataliyar dakarun kiyaye zaman lafiya ta kasashen nahiyar Africa ke fuskanta,wanda hakan ala tilas ya haifar da saka su a cikin laimar dakarun Mdd dake yankin.

Anan ya kara da cewa ya zama dole dakarun kiyaye zaman lafiyar na Mdd, suyi amfani da karfin soji wajen kare lafiyar Al´ummar yankin.

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun shaidar da cewa wannan rikici na Darfur daya ki ci yaki cinyewa ya dai dai ta mutanen yankin kusan miliyan biyu.