1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan rikicin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniNovember 16, 2007
https://p.dw.com/p/CIBw

Mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka, Mr John Negroponte, ya isa ƙasar Pakistan. A lokacin ziyarar Mr Negroponte, zai yi ƙokarin janyo hankulan mahukuntan ƙasar ne ɗage dokar ta ɓaci da su ka kafa.Wakilin na Amirka zai kuma yi ƙokarin ganawa da ɓangarorin ´Yan adawa na ƙasar, da zummar samo bakin zaren warware rikicin siyasa da ƙasar ke fama da shi a halin yanzu. Zuwan na Mr Negroponte yazo ne dai-dai da lokacin da aka sako shugabar adawa ta ƙasar, Benazir Bhutto ne daga ɗaurin talala da akayi mata.kafafen yada labarai sun rawaito Bhutto na jaddada aniyarta na ci gaba da Gwagwarmaya a ƙasar.

Benazir Bhutto ta ce Babu wata tattaunawar sulhu a tsakaninmu da Musharraf, domin al´umma sun dawo daga rakiyarsa, wanda duk kuwa ya kusance shi shi ma farin jininsa ka iya dusashewa.Tuni dai tsoffin Faraministocin ƙasar biyu, wato Benazir Bhutto da Mr Nawaz Sharif suka cimma yarjejeniyar kalubalantar Mr Musharraf, a fagen zaɓen gama garin.