1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan matsalar bakin haure

November 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buao

A yau aka bude taron wuni biyu , a tsakanin wakilan kungiyyar Eu dana kasashen Africa, a can birnin Tripoli na kasar Libya.

Taron , wanda ke zaman irin sa na farko, zai mayar da hankali ne kann matsalolin bakin haure daga kasashen Africa izuwa nahiyar turai.

Ana dai sa ran a karshen taron wuni biyun, mahalarta taron zasu fitar da yarjejeniya da suke fata ta zama ta karshe, a kokarin dakile wannan matsala da taki ci taki cinyewa