Kokarin sauya akidar tsofaffin ′yan Boko Haram | Siyasa | DW | 11.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin sauya akidar tsofaffin 'yan Boko Haram

Sabobbin dabarun da suka hada da wa'azi da koyar da sana'o'i sannan da kokarin sauya tunani, na daga cikin burin kawo karshen tada hankali da makamai da matsalar ta ta'addanci a Najeriya.

A yayin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke shirin tuhumar wasu a cikinsu, mafi karkata na tunani game da makomar 'yan kungiyar na zaman sauya musu ra'ayi tare da wankesu daga akida ta tsanar da ta kaisu ga aikin na ta'addanci.

Abin kuma da ranar yau ya kai gwamnatin kasar da hadin Kungiyar Tarrayar Turai fitar da wani sababbi na dabarun sauya tunanin a tsakanin dubu dubatar yan ta'adda na kasar.

Sabbin dabarun da suka hada da wa'azi, da koyar da sana'o'i sannan da kokari na sauya tunani dai na da burin kai karshen tada hankali da makaman da ke zaman ruwan dare a cikin matsalar ta ta'addanci.

Nigeria Soldaten in Damboa

Rundunar sojin Najeriya a flin daga

Kasar ta Najeriya na fatan sabuwar dabarar dake zaman irinta ta farko a kokari na sauyin ra'ayi za tai tasiri wajen kai karshen matsalar da ta dauki yankin na arewa maso gabas ta dora ta a taswira ta taáddanci.

Kuma tuni a fadar Steve Abana da ke zaman shugaban kula da sauya akidar tada hankali a offishin mashawarcin tsaron kasar, aka fara ganin alamun nasara yanzu.

"A yanzu muna da 'yan kurkuku 45 da ake zargi da zama 'yan kungiyar Boko ta Haram a gidan yari na Kuje, kuma a ciki 42 sun amince a kashin kansu su shiga cikin wannan shiri na sauya tunani kaiga babbar nasara ce. Kuma a cikinsu kotu ta sallami kusan hudu zuwa biyar kuma sun koma a cikin alúmmarsu suna waázin sauyi mai kyau. Kuma muna amfani dasu a matsayin zakaran gwajin dafin da ke nuna irin nasarar tsarin".

Sabon tsarin da ya zo dai dai lokacin da daruruwa na ya'yan kungiyar ke zubar da makamai da ma mika wuya dai na iya yin tasiri wajen kakkabe burbudin matsalar a tsakanin alúmmar yankin Arewa maso Gabas da ke fuskantar dar dar a sabuwa ta rayuwa a gidajensu.

Wani malamin da ke cikin shirin waázi ga kammamun na kungiyar ta Boko Haram amma kuma bai so a baiyyana sunansa ba dai ya ce sannu a hankali su na nasarar sauya tunanin da ya kaisu ga daukar makamin can baya.

Nigeria Armee Soldaten

Rundunar tsaron Najeriya

To sai dai koma ya zuwa yaushe ne dai hukumomin kasar ta Najeriya ke iya kai karshen tasirin malam a tsakanin yaran malam din dai, shirin da ke zaman na hadin gwiwa a tsakanin Tarrayar Turai da ofishin mashawarcin tsaron kasar sannan kuma ke mai da hankali kan daurarru na gidan yari dai na daukar fasalin wani taron kasa da kasa a birnin Ankara na kasar Turkiyya kan matsala.

Kuma a fadar Richard Young da ke zaman mataimakin jakadan Tarayyar Turai a kasar ke da babban tasirin sauya makomar daruruwa na 'yan da ke mika wuya a kusan kullum.

"Akwai daruruwa ko kuma dubban wadanda ke cikin tada kayar baya, kuma ke da tunani na tada hankali, kamar yadda muka gani a kwanakin nan, sanarwar kakakin soja cewar akalla 800 sun mika wuya. To maganar ita ce ya zaka yi da wadannan mutane".

Abin jira a gani dai na zaman tasirin sabon shirin ga makomar yakin da ke nuna alamun karewa a cikin sauri.

Sauti da bidiyo akan labarin