1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sarrafa alluran riga kafin murar tsaunye wa mutane

February 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuRc

Hukumar kula da lafioya ta mdd ta sanar da samun dumbin nasara a kokarinta na ganin cewa an alluran riga kafin kamuwa da cutar murar tsuntsaye wa mutane,domin gudun illar da cutar zata haifar idan har ta saje da jikin mutane ,wadda zata jagoranci yaduwa daga mutum zuwa mutum.Sai kawo yanzu hukumar kula da lafiyan ta bayyana cewa kasashen duniya basu da sukunin samarda isassun magungunan,sduk da cewa likitoci masu bincike sunyi nuni dacewa baa tabbatar da tasirin alluran a jikin mutane ba.Hukumar dai a halin yanzu haka tana tattaunawa da masanaantu 16 dake sarrafa alluran a kasashe 10,da zasu yaki cutar da H5N1.