1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samun masalaha a rikicin Lebanon

August 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buo5

Shugabannin kasashe na duniya na cigaba da kokari domin samun masalaha ta kawo karshen rikicin yankin gabas ta tsakiya. P/M Britaniya Tony Blair yace hanya daya tilo ta samun masalaha ita ce kwance damarar dakarun Hizbullah. Ita ma a nata bangaren sakatariyar´harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta baiyana fatan cimma daidaito a tsakanin kasashe domin kawo karshen rikicin a cikin wannan makon. A waje guda kuma Washington ta baiyana rawar da Syria zata iya takawa wajen shawo kan rikicin tsakanin Israila da Lebanon. Wanan dai matashiya ce ga tuntubar da ake fatan samu tsakanin Washington da Damascus a kan wannan batu.