Kokarin samo naura da zata sanarda abkuwar Tsunami | Siyasa | DW | 04.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin samo naura da zata sanarda abkuwar Tsunami

UNESCO ta fara yunkurin samarda naurar karkashin teku da zata baiyana tsunami na tafe

.:Wakilai daga kasashe 27 da ke bakin iyakar tekun India suka hallara domin tattauna shirin samarda tsarin kasa da kasa na gano tsumani tun kafin abkuwarsa,wanda ake sa ran kaddamar da shi daga nan zuwa watan yuli na 2006.

Wannan naura dai zata bada wata alama kafin abkuwar tsunami tare da jiniya da zasu sanarda jamaa cewa tsunami na tafe.

Babban sakataren hukumar kula da harkokin ruwa ta kasa da kasa na UNESCO,Patricio Bernal,ya ce taron na wannan mako da farko zai duba batun fasahar kera wannan naura.

Tuni dama tekun na India na da naurori masu karfi da suke bada bayanai game da abubuwan da suke faruwa a cikin teku,amma kara inganta aiyukan wadannan naurori zai taimaka su gano tsunami tun kafin abkuwarsa.

Tekun Pacific yana da shima na shi naura na kasa da kasa da ka iya hango tsunamin,da aka girke Honolulu fiye da shekaru50.Patricio Bernal na UNESCO ya ce batun inganta naurar da ke tekun India ya tashi ne a bara bayan ambaliyar rura ta tsunami ta halaka akalla mutane 250,000 a kudanci da kuma kudu maso gabashin Asiya.

Bayan balain tsunami na bara,an samu taimako na kudi da kuma alkawurra da dama na taimaka kafa irin wadannan naurori musamman ma a tekun India to sai dai Patricio Bernal ya ce gano ko kuma hango cewa tsunami na tafe ba a nan ta tsaya ba.

An shirya zaa gudanar da taro akan ci gaba da aka samu,a bwatan disamba mai zuwa a birnin Hydrebad na kasar India.