1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin samarda naurar bada bayanai

Zainab MohammedDecember 24, 2007

Kwararrun Jamus sun kusan cimma buri

https://p.dw.com/p/CfoQ
Naurar gano bayanaiHoto: dw-tv

Ƙwararru ta fannin ilimin kimiyya dake nan tarayyar jamus na cigaba da kokarin ganin cewar sun gano hanyar da za a yi gargaɗin gaggawa idan bala’i kamar na igiyar ruwa na tsunami ya sake aukuwa.

Ayayin da ya rage yini guda da cika shekaru uku da kewayowar ranar da alummomin kasar Indonesia suka fuskanci balain igiyar ruwa na tsunami,daya haddasa asaran rayuka masu yawa,kwararru ta fannin kimiyya dake nan jamus na kokarin cikanta alkawarin da suka dauka na gano wani gargadin gaggawa ga alumma.

Jaamii a cibiyar Nazarin harkokin bincike dake birnin Postdam a nan jamus,Joern Lauterjung,yace makasudun hakan shine domin samar da gargadin gaggawa a minituna 10 karshe na aukuwan girgizar kasa da zai shafi igiyar ruwa,domin kare asarar rayuka.

Jamus dai ta dauki alkawrin samar da wannan naura maunin kasa da igiyoyin ruwan da zai bayar da bayanai na gaggawan ne ta hanyar Satellite zuwa naurar yanar gizo gizo ne,kwanaki 4 da aukuwar balaiin igiyar ruwa na tsunami ,wanda ya kashe mutane dubu 220 a tsibirin Balin kasar Indonesia ,a ranar 26 ga watan Disamban 2004.

Gwamnatin Indonesian dai tayi maraba da wannan yunkuri na Jamus,inda daga nan ne kwararru ta fannin kimiyya jamusawa 120 suka kaddamar da wannan bincike.Shirin dai anyi masa lakabi da sunan gudummowan Jamus tsarin wajen gargargadin gaggawa dangane da barazanar igiyar ruwa ta tsunami.

Shekaru uku bayannan kwararru sun kusan cimma burin su,inda suka sanar da fatan tsarin zai fara aiki a watan Nuwamban 2008.

Tun daga farkon shekara ta 2005 nedai,tawagar jamusawan suka fara aiki tare da Jamian Indonesi dana Amurka dana Japan,na kafa tashoshin gwajin igiyoyin ruwa dake kan kasa dake karkashin Teku.

Sanin inda igiyoyin ruwan suke kwace dai iniji kwararrun yanada muhimmanci a samun nasarar wannan tsarin, kasancewar naurorin dake kan kasa bazasu bayar da ainihin yadda igiyoyin ruwan dake tekun suka salace ba,idan aka samu girgizar kasa.

Bugu da kari sai igiyoyin ruwan sun samu mummunan lahani ne daga girgizar kasa ne zai iya kasancewa tsunami.Wadannan naurorin dai bayan an hada su,zaa sanya su ne karkashin teku,wadanda zasu iya tafiyar km 5 zuwa karkashin ruwan.Naurorin zasu iya gwajin karfin ruwa dake cikin teku da kuma nisan sa zuwa sama.Hakan na nufin naurorin zasu iya bayyana duk wani sabati ko matsala data ritsa da igiyoyin ruwan nan take.Kuma wannan gwajin zai gabatar da bayanai ne cikin dukkan dakikai 15,wadda zata aike zuwa cikin Jakarta ta hanyar Satellite.