Kokarin samar da sabuwar gwamnati a Maroko | Labarai | DW | 26.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin samar da sabuwar gwamnati a Maroko

Bayan watanni biyar ba tare da samun daidaito wajen kafa sabuwar gwamnati ba, sabon Firaministan da aka bai wa wannan mukami a tsakiyar wannan wata ya ce tattaunawar ta kawo karshe.

Saad-Eddine El Othmani Außenminister Marokko (Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images)

Sabon Firaministan kasar Maroko Saad-Eddine El-Othmani

Firaminista Saad-Eddine El-Othmani ya ce ba da dadewa ba za a fitar da jerin sunayen sabbin membobin gwamnatin da za ta kunshi mutane daga jam'iyyu shida na hadaka. Sabuwar gwamnatin ta Maroko za ta kunshi 'yan jam'iyyar PJD (Parti justice et Developpement), da abokiyar kawancenta jam'iyyar PPS ta masu ra'ayin kwaminisanci, da jam'iyyar RNI ta masu sassaucin ra'ayi, da jam'iyyar "Mouvement Populaire" MP, da "Union Constitutionnelle" ta UC da kuma jam'iyyar USFP ta 'yan Socialiste, a cewar Firaminista El-Othmani yayin wani taron manema labarai a birnin Rabat. Firaministan ya kara da cewa a wannan Lahadin ne za a kafa kwamitin da zai dukufa wajen zaben sabbin ministocin da kuma rubuta tsarin tafiyar da harkokin gwamnatin.