1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin nemo sabon sakataren Mdd

A mako mai zuwa ne ake sa ran Mdd zata amince da MR Ban Ki Moon a matsayin sabon sakataren Mdd.

Hakan dai ya biyo bayan samun nasara ne da yayi a wata kuri´ar bayan fage da aka kada a majalisar har sau hudu ne.

Jim kadan da kada kurí´ar ta karshe rahotanni sun rawaito jakadan Amurka a Mdd, wato John Bolton na cewa mutum ne daya dace da wannan mukami.

A yan kwanaki kadan masu zuwa ne ake sa ran Mdd a hukuamnce zata kada kuri´ar amincewa da ministan harkokin wajen na Koriya ta kudu a wannan sabon mukami.

Kokarin neman sabon sakataren mdd dai ya biyo bayan karewar wa´adin Mr Kofi Anan ne akan wannan mukami, a karshen wannan shekara da muke ciki.