Kokarin neman mafita kan rikicin kasar Burundi
July 14, 2015Talla
Wannan aiki na shugaba Museveni da kungiyar EAC ta kasashen gabashin Afirka ta dora masa bayan rishin samun nasara a tattaunawar da aka yi a baya, na zaman mai wahalar gaske ganin yadda bengarorin kowa ya kife kan bakansa. A cewar Léonce Ngendakumana, daya daga cikin kusoshin adawar kasar ta Burundi, suna jiran abubuwa da dama daga Shugaba Museveni, ba wai a matsayinsa na mai shiga tskani ba kawai, a matsayinsa na mai kare yarjejeniya birnin Arusha wanda yake daya daga cikin wadanda suka kirkirota.