Kokarin murkushe ′yan jarida a Turkiya | Labarai | DW | 27.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin murkushe 'yan jarida a Turkiya

Bayan kwashe tsahon kwanaki 13 a kwamar jami'an 'yan sandan Turkiya, dan jaridar nan na Jamus Deniz Yucel ya gurfana a akron farko a gaban kuliya.

 Deniz Yucel dan jaridar Jamus da mahukuntan Turkiya suka tsare

Deniz Yucel dan jaridar Jamus da mahukuntan Turkiya suka tsare

Jaridar Die Welt ta Jamus wadda a nan ne Yucel kewa aiki yayin da 'yan sanda suka cafke shi a Turkiyan, ta tabbatar da gurfanar tasa a gaban kuliya. Yucel dai na rike da fasfo biyu na kasashen Jamus da Turkiya, kuma yana zaman dan jaridar Jamus na farko da jami'an 'yan sandan na Turkiya suka tsare a wani bangare na kokarin murkushe 'yan jaridu da kasar ke yi, tun bayan da mahukuntanta suka sanya dokar ta baci sakamakon yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da ta fuskanata a shekarar da ta gabata ta 2016.