Kokarin kwace birnin Mosul daga IS | Labarai | DW | 03.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kwace birnin Mosul daga IS

Fafatawar da ake ci gaba da yi tsakanin dakarun Iraki da kuma mayakan IS a kokarin kwace birnin Mosul ya haddasa karuwar fararen hula da ke tserewa domin tsira da ransu.

Gumurzu domin kwace birnin Mosul na Iraki

Gumurzu domin kwace birnin Mosul na Iraki

Rahotanni sun nunar da cewa ana can ana ci gaba da gwabza fada a yammacin birnin na Mosul tsakanin dakarun Iraki da ke samun goyon bayan mayakan sa kai na Musulmi mabiya mazhabar Shi'a da kuma 'yan ta'addan IS. Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ruwaito cewa daga makon da ya gabata kawo yanzu, 'yan gudun hijira 30.000 ne suka isa sansanonin 'yan gudun hijirar ciki kuwa har da kananan yara 15.000, inda tuni asusun na UNICEF ya yi musu rijista kamar yadda jagoran asusun a birnin Erlib Bastien Vigneau ya tabbatar. Tun dai fara fafatawar ta kwace birnin Mosul cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2016 kawo yanzu, fararen hula 191,000 ne aka kiyasta cewa sun kauracewa yankin na Mosul. Kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa akalla mutane 800,000 ne ke zaune a yankin yammacin birnin na Mosul, da ke zaman yanki na karshe da kungiyar ta IS ke da karfi a Irakin.