1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kula da 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 3, 2016

Mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU sun amince da bayar da kimanin biliyan uku na kudin euro domin tallafawa 'yan gudun hijira a Turkiya.

https://p.dw.com/p/1HpRl
'Yan gudun hijira da ke kaura zuwa Turai
Miliyoyin 'yan gudun hijira ne a 'yan shekarun nan suka yi kaura zuwa TuraiHoto: Getty Images/J. J. Mitchell

Wannan makudan kudaden dai za a yi amfani da su ne domin inganta rayuwar 'yan gudun hijirar da ke zaune a Turkiya, wanda a cewarsu za su taimaka wajen rage tururuwar da suke yi wajen shigowa nahiyar Turai ko ta halin kaka domin samun ingantacciyar rayuwa. Nahiyar Turai dai na fama da matsalar kwararar 'yan gudun hijira da ke neman mafaka wadanda aka kiyasta cewa sama da miliyan guda ne suka ketara zuwa Turan. Da damansu dai sun kauracewa yakin da ake fama da shi ne a Siriya.