Kokarin kawo sulhu a tsakanin Sudan da Chad | Labarai | DW | 27.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kawo sulhu a tsakanin Sudan da Chad

Mahukuntan Sudan dana Chadi sun rattaba hannu akan yarjejeniyar warware takaddamar da suka fuskanta a kwanakin baya, a iyakar data raba kasashen biyu.

Dukkannin kasashen biyu sun amince da warware wannan takaddama ta hanyar diplomasiyya. To sai dai ya zuwa yanzu babu wata yarjejeniya da kasashen biyu suka cimma na jibge dakarun soji na da zasu dinga sintiri a iyakar juna.

A can baya dai idan za a iya tunawa kasashen biyu sun soki lamirin juna na taimakawa yan tawaye cin karen su babu babbaka, musanmamma a yammacin yankin Darfur dake Kasar Sudan