Kokarin kawo karshen rikicin yankin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 21.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kawo karshen rikicin yankin gabas ta tsakiya

Kasashen Russia da Amurka da kuma wakilan kungiyar Eu dana Mdd na shirin gudanar da wani taro, a birnin Berlin na tarayyar Jamus,akan rikicin YGT.

Taron wanda ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeir ke daukar bakoncin sa, ana sa ran zai kuma samu halartar Sakataren Mdd Mr Baki Moon.

Rahotanni dai sun rawaito sakatariyar harkokin wajen Amurka CR na shirin bukatar taron, kin yarda da gwamnatin hadin kann yankin Palasdinu, har sai idan sun yarda da kasancewar kasar Israela.

Ana dai sa ran wakilan wannan taro, zasu duba hanyoyin dawo da daftarin zaman lafiyar nan na gabas ta tsakiya cikin hayyacin sa, da nufin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.