Kokarin kakabawa Iran wani takunkumi | Labarai | DW | 02.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kakabawa Iran wani takunkumi

Kasashen dake fada aji a duniya sun hallara a birnin London don tattauna mataki na gaba da zasu dauka kann Iran. Akwai dai hasashen cewa kasashen na tunanin kakabawa kasar ta Iran wani takunkumin ne, dake a matsayin na uku cikin jerin matakan ladaftarwa da ake dauka akan kasar.Tattaunawar dai a cewar rahotanni na gudana ne a tsakanin wakilan kasashen Amurka da Russia da China da Biritaniya da Faransa a waje daya kuma da Jamus.Bayanai dai sun nunar da cewa daukar wannan hukunci na gaba, yazo ne bayan da kasashen suka fuskanci cewa kasar ta Iran har yanzu na ci gaba da sarrafa sanadarin ta na Uranium. Kasashen na yamma dai na zargin cewa Iran din na kokarin kera makami ne na kare dangi, to amma Iran din ta musanta hakan da cewa shirin na inganta hasken wutar lantarki ne ga yan kasar.